Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka mai Jiran Gado Barack Obama,zai Maye Gurbin Wasu Manyan Jami'an Ayyukan Lelen Asiri Biyu Cikin Watan Janairu


Wata Jaridar Amurka ta bada labarin Shugaban Amurka Mai Jiran Gado Barack Obama,zai sake manyan kusoshi ayyukan leken asiri biyu, Idan ya kama aiki cikin watan Janairu.

Jaridar "Washington Post" ta ambaci wasu Jami'an aikin leken asiri suna cewa Darektan cibiyar leken asiri ta kasa,Mike McConnell,da Darektan Hukumar Leken Asiri Ta CIA, Michael Hayden,akwai wasu wakilan Majalisa 'Yan Democrat masu fada aji da basa goyon bayansu.

Jaridar tace wakilan Majalisa suna fushi da goyon bayanda Jami'an biyu suke bauwa shirin gallazawa mutane da ake tuhuma da ta'addanci lokacinda ake musu tambayoyi,da kuma shirin kasa kunne ga masu magana ta tarho da gwamnatin Shugaba Bush take aiwatarwa. Jami'ai dake cikin kwamitin tsara shirin mika Mulki na Obama,sun gayawa jaridar cewa babu shawara da aka yanke gameda ko wani mukami a bangaren ayyukan leken asiri.

Jiya Talata jagoran kwamitin tsara karbar mulki na shugaba mai Jiran Gado Obama,ya bayyana manufofin Obama kan 'yan kamasho masu wakiltar kamfanoni da wasu muradu,a lokacin mulkinsa.

XS
SM
MD
LG