Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Marawa Al-Bashir Baya A Rikicin Sa Da Kotun Duniya


Shugaba Hu Jintao na kasar Sin, ya baiyana cikakken goyon bayansa ga kasar Sudan da Shugabanta Omar Hassan Al-Bashir, wanda ke fuskantar tuhumar kisan kare dangi daga Kotun Kasa da Kasa.

A yau Laraba Shugaba Hu ya bayar da wata sanarwa dake baiyana cewa Sudan da China sun share shekaru hamsin suna da huldar diplomasiyya ta kut da kut.

Mr. Hu yace China tana mutunta diyaucin kasar Sudan, da kuma 'yancin ta na kare iyakokin kasar ta, ya kuma ce yana goyon bayan dukkan hanyoyin maslaha da za a bi domin sulhunta jama'ar kasar.

China ita ce ke sayen kaso mafi yawa na man fetur din da Sudan ke fitarwa.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun sha sukan kasar China, kan yadda ta kauda idonta daga yadda man da take saye daga wajen sudan ke taimaka mata ta ci gaba da yakar 'yan tawayen yankin Darfur.

Masu gabatar da kara na Kotun Kasa da Kasa sun zargi Shugaba Al-Bashir da ta'azzara yanayin fyade, kisan gilla, da cin zarafin mazauna yankin Darfur, sun kuma bukaci kotun da ta bada takardar sammaci domin a kamo shi.

XS
SM
MD
LG