Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Tabbatarda Mutuwar Mutane Goma Sha Uku A zangarda Akayi A Tibet


China tace adadin wadanda suka halaka a Lhasa, fadar yankin Tibet ranar Jummaa, sakamakon zanga Zangar lumana kan kyamar mulkin China a yankin,da daga bisani ta kazance.Yanzu hukumomin China sunce mutum goma sha ukune suka mutu. Ahalin yanzu Gwamnatin China ta zafafa cacar baki tsakaninta da shugaban addinin Budda na Tibet dake gudun hijira, Dalai lama.

Haka kuma Jami’an hukumomin wasanni daga kasashe dake Tarayyar Turai suna nuna adawa da masu neman a kauracewa wasannin Olympics na bana da zaayi a Beijing,yayinda ake kallon yadda China take kokarin shawo kan zanga zangar a Tibet.

Da yake magana gabannin taron Jami’an Hukumar Wasanni na Tarayyar Turai a yau a Slovenia,Ministan wasanni na Slovenia, Milan Zver,yace baya goyon bayan a kauracewa wasannin Olympics din. Haka kuma yace zaiyi wuya ace batun neman a kauracewa wasannin bazai taso ba lokacin taronda zasuyui.A yau Rasha ta shiga sahun kasasshe dake nuna rashin goyon bayan akauracewa wasannin Olympics din domin abinda yake faruwa a Tibet.Sanarwa daga MHWR a yau tace zanga zanga a Tibet, harka ce ta cikin gidan China,daga nan tayi suka ga wadanda tace suke kokarin tsoma siyasa cikin harkar Olympics.

Hukumar wasannin Olympics ta kasa da kasa tace 'yanwasa da dama ne suka nuna aniyar kauracewa wasannin Olympics da zayi a Beijing saboda rashin jin dadin ganin yadda China take murkushe masu gwagwarmaya a Tibet.

XS
SM
MD
LG