Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane Tara A Iraq


Majiyoyin sojojin kasar Iraki sun ce yau talata wani dan harin bam din kunar bakin wake ya afkama wata bas(motar Safa) da ke fitowa daga birnin Mosul a arewacin kasar, harin da ya janyo asarar rayukan akalla mutane tara. Rahotannin farko sun ce dimbin mutane sun jikkata. Sojoji sun ce bas din kasar Syria ta tasamma zuwa.

A wani labari, ma’aikatar tsaron Amurka ta ce duk da cewa za’a janye sojojin Amurka kimanin dubu ishirin a tsakiyar shekarar nan, wasun su masu yawan gaske za su ci gaba da zama a kasar Iraki fiye da yadda su ke kafin a kara yawan su a bara.

Babban mai kula da ayyukan sojin da sunan babban hafsan hafsoshin rundunonin mayakan Amurka, laftana janar Carter Ham, ya ce ya na hasahen cewa a watan yuli za’a samu sojoji kimanin dubu dari da arba’in.

karin yawan sojoji dubu takwas kenan fiye da lokacin da shugaba Bush ya bada umarnin kasar ta tura sojoji Iraki a shekarar dubu biyu da bakwai da nufin rage tashin hankali da kuma zafafa neman dinke barakar siyasar da ake fama da ita a kasar.

XS
SM
MD
LG