Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Darfur: Sudan Ta Rungumi Kaddara


Sudan tace ta amince da kudurin Majalisar Dinkin Duniya dake kan aikewa da dakarun hadin guiwa, domin kiyaye zaman lafiya a yankin Darfur, wanda yaki ya daidaita.

Da yake magana da manema labarai a birnin Khartoum a yau, Ministan Harkokin Wajen Sudan, Mr. Lam Akol yace Sudan ta gamsu da kudurin, kuma zata bada dukkan hadin kan da ake bukata domin tabbatar da nasarar shirin.

Sudan ta shafe watanni tana adawa da shirin, yayin da kasashen duniya suka ci gaba da iza mata wuta. Babbar kungiyar ‘yan tawaye dake yankin na Darfur, wato SLM, tace wannan kuduri yayi mata dadi.

Saidai wani kakakinta Yahiya Bolad yace kungiyarsa ba zata yi saurin yabon dan kuturu ba, sai ta gani karara, dakarun suna aiwatar da aikinsu na kiyaye zaman lafiya, sannan zata fito da matsayin karshe.

XS
SM
MD
LG