Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Talata Za Fara Sabon Zagayen Taron Daunin Ikon Zimbabwe a Afrika Ta Kudu.


Shugabannin Afrika ta kudu sun bada sanarwar shirya wani sabon zagayen shawarwarin daunin ikon Zimbabwe,suna kuma gargadin cewa al'amuran rayuwa a Zimbabwe suna kara tabarbarewa.

Da yake magana yau litinin a Johanesberg, shugaban Afirka ta kudu Kgalema Motlanthe yace halin rayuwa a Zimbabwe zai kara muni,idan kasar bata kafa Gwamnati halaltacciya ba. Motlanthe yace wakilai daga Jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin Zimbabwe da kuma na rassan MDC 2 masu hamayya za su gana gobe Talata tareda mai shiga tsakani tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki.

Shawarwari gameda daunin iko ya cije na watanni,yayinda ake kara nuna damuwa kan karancin abinci a kasar da kuma tabarbarewar kiwon lafiya.

XS
SM
MD
LG