Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dick Cheney Ya Kai Ziyarar Ba Zata A Iraqi


Mataimakin shugaban Amurka Dick Cheney wanda a halin yanzu yake Bagadaza,yace a goyon bayan da Amurka take baiwa Iraqi, babu gudu babu ja da baya. Cheney ya fadi haka ne a yau bayan ganawarsa da Frime Minista Nouri al-Maliki.Shugabannin biyu sun tattauna kan ci gaba da aka samu kan ingantuwar tsaro a kasar da wasu batutuwa na daban.

Yau litinin ce Cheney ya isa Bagdaza a ziyarar ba zata da ya kai can. Da farko ya fara ganawa ne da babban kwamandan Amurka a Iraqi, Janar David Petreaus. Jim kadan da isarsa ne wata mummunar fashewa ta auku a Bagadaza,amma babu cikakken bayani.

Yada zango da Mr. Cheney yayi a Bgadaza, yana cikin rangadi da yake yi a Gabas ta Tsakiya,da zai kaishi Oman,Saudiyya,Isra’ila,yammacin kogin Jordan da kuma Turkiyya.

Dan Majalisar Dattijan Amurka, wanda kuma ake sa ran shine dan takarar shugabancin Amurka a zaben bana John McCain,shima yana Iraqi domin abinda ya kira ziyarar gane ma ido.Haka shima ya gana da Frime Minista Nouri al-Maliki.

XS
SM
MD
LG