Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Tana Nazarin Bukatar Tura Karin Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya A Kwango


Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yana nazarin kira da babban sakataren Majalisar Banki Moon yayi, na neman ya tura karin sojojin kiyaye zaman alfiya a Kwango.

Babban Sakataren Majalisar Mr. Banki Moon yayi kira da tura karin sojoji dubu uku domin agawaza wadanda ke can da aiki yayiwa yawa a gabashin Kwango,yana cewa lamarin yana kara tabarbarewa.

Yace fada tsakanin sojojin Gwamnati da 'yan tawaye ya hana kai agaji ga mutane fiyeda dubu dari da yakin ya raba da muhallansu. Ana sa ran kwamitin zai dauki mataki kan bukatar da Mr. Ban ya gabatar masa nan da karshen watan nan.

Jami'an Majalisar dinkin Duniya sunce ahalin yanzu akwai sojojin Majalisar Dinkin Duniya dubu 17 a Kwango,akasarinsu suna gabshin kasar inda ake fama da tashe tashen hankula.

Majalisar Dinkin Duniya tana zargin sojojin Gwamnati da yin fyade ga farar hula da dibar ganima a kauyuka dake yankin. Wani kakakin Majalisar Dinkin Duniya yace galibin hare haren suna aukuwa ne a yankunan Kanyabayonga,dake arewacin babban birnin lardi Goma.

XS
SM
MD
LG