Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk da Karin Matakan Tsaro Da Aka Dauka a Bagadaza An Kashe Akalla Mutane Goma Sha Uku


Jami’an Iraqi sunce an kashe mutane akalla 13 a unguwar Sadr ta birnin Bagadaza duk da karin matakan tsaron da aka dauka a ranar cikar shekaru biyar da faduwar Bagadaza ga sojojin Amurka.

’Yan sanda sun ce wani abu ya fashe ya kashe mutane 7 ya raunata wasu fiye da 14 a unguwar ta ’yan mazhabin Shi’a. A cikin dare kuma, kwanson bam ya kashe mutane akalla 6, ya raunata wasu akalla 24. Ba a san ko wanene yake da alhakin kai hare-haren ba. An samu karuwar fada a wannan unguwa a tsakanin sojojin Amurka da mayaka masu yin biyayya ga shaihin malami na Shi’a Moqtada al-Sadr.

A wani lamarin dabam, rundunar sojojin Amurka ta bada sanarwar mutuwar karin sojojinta biyu, abinda ya kawo adadin sojojin nata da aka kashe zuwa 13 tun daga ranar lahadi.

A yau laraba, gwamnatin Iraqi ta kafa dokar hana fita waje a duk fadin Bagadaza, daga karfe 5 na asuba har zuwa 12 na dare.

XS
SM
MD
LG