Shugaban Amurka mai jiran Gado Barack Obama a yau litinin ya zabi shugaban Bankin Tarayya,reshen New York,Timothy Geithner, a matsayin sakataren Baitulmalinsa(watau ministan kudi), yayinda tsohon sakataren baitulmali Lawrence Summers zai zamo Shugaban Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa.
Getihner ya taka ruwa da tsaki a kokarin gwamnatin shugaba Bush na ceto kasuwannin hada-hadar kudi.Mr. Obama ya ce Geithner,yana da masaniya ta musamman gameda wannan matsala