Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Mai Jiran Gado Ya Gana Da Masu Bashi Shawara Kan Harkokin Tattalin Arziki


Shugaban Amurka Mai jiran gado Barack Obama, a yau Juma’a ya gana da tawagar jami‘an shirya tsarin tattalin arziki a birnin Chicago, sannan a yau ɗin yake shirin gabatar da tattaunawarsa ta farko tareda manema labarai tun samun nasarar da yayi a zaɓen shugaban ƙasar Amurka.

Makonni goma suka rage a rantsar da Obama sabon shugaban ƙasa, amma zai gaji babbar matsalar rinchaɓewar tattalin arzikin Amurka irinsa na farko tun afkuwar talauchin Amurka shekaru da dama da suka gabata.

Nan bada jimawa ba ake sa ran Barack Obaman zai bayyana sunan sabon sakataren Baitul malin Amurka. Jiya Alhamis ya naɗa sabon babban jami’in kula da ayyukan fadar shugaban ƙasa Rahm Emanuel wanda tuni har ya amsa gayyatar da aka yi masa, daman ya taɓa yin irin wannan aikin a zamanin shugaba Bill Clinton, a yanzu haka kuma ɗan majalisar wakilai ne daga mazaɓar Illinois.

XS
SM
MD
LG