Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Dakon Sakamakon Zabe,Domin Sanin Wa Zai Gaji Shugaba Gerge Bush.


Amerkawa masu kaɗa ƙuri‘a yau Talata sun fita sun kaɗa ƙuri‘a a zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisar dokoki.

Yanzu jiran da ake yi shine sakamakon zaɓen da zai samar da wanda zai gaji shugaba Bush a tsakanin John McCain na jam’iyyar Republican da Barack Obama na jam’iyyar Democrat. Anga dogayen layin masu kaɗa ƙuri‘a a jihohin Amurka dadama musamman a jihohin Virginia da kuma nan Gundumar Colombiya da kuma Maryland dake maƙwabtaka da ita.

Masu fashin baƙin siyasar Amurka sun bayyana cewar idan Barack Obama aka zaɓa shine ke nan baƙar fatar Amurka na farko da zai zama shugaban Amurka. Idan kuma John MCcain aka zaɓo, shine ke nan dattijo mai shekaru 72 da haihuwa a karon farko da yayi takara kuma ya sami nasarar zama shugaban Amurka a tarihin Amurka. Kazalika mai mara masa baya Sarah Palin zata zama macen farko da zata hau muƙamin mataimakiyar shugaban Amurka. Haƙiƙa zaɓen yau yana da muhimmancin gaske a tarihin siyasar Amurka.XS
SM
MD
LG