Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fada Tsakanin Mayakan sakai Na Mahdi Da Dakaru A Basra Ya Kashe Akalla Mutane Goma Sha Biyu


Babban malamin nan na ’yan Shi’a Moqtada al-Sadr yayi barazanar shiga tawaye a duk fadin kasar yayinda jami’an tsaro ke ci gaba da gumurzu da mayakan Mahdi Army masu biyayya ga malamin.

Cikin wata sanarwa da dogarawan Sadr suka karanta yau, tace, malamin zai shiga tawayen muddin ba a daina kaiwa ’yan kungiyarsa hari ba.

Jami’an Iraq sun ce kazamin fadan da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da mayakan sakai yan Shi’a a kudancin birnin Basra ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane goma sha biyu, sha takwas kuma suka jikkata yau, ranar farko da kai harin soji kan mayakan sa kan dake kudancin kasar.

Shaidu sun bayyana jin karar bindiga da kuma hangen hayaki na tashi a wasu sassan birnin jim kadan da fara bata kashin. Yan sanda sun kafa dokar ta baci yau a birane da dama na kudancin ƙasar. Yayinda aka kafa irin wannan dokar a duk fadin lardin Basra.

Ana kuma kai ruwa rana a Bagadaza babban birnin kasar tsakanin mayakan Mahdi da membobin wani bangaren ’yan Shi’an.

XS
SM
MD
LG