Shugabar Hukumar Kula da hakkin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya tace kawanya da Israila take yiwa Zirin Gaza tana hana mazauna yankin hakkin da ya wajaba a baiwa ko wani bil'adama.
Kwamishina Mai kula da hakkin Bil'adama ta MDD,Navi Pillay, yau Talata tayi kira cikin gaggawa ga Isra'ila da ta janye killace yankin da tayi.Bayan haka sai a fara aikin jinkai mai karfin gaske domin saukaka abinda ta kira mummunar matsin rayuwa da mazauna Gaza suke fama dashi.
Pillay tace mutane miliyan daya da rabi dake zaune a Gaza an hanasu hakkinsu wadda kai tsaye ya saba dokokin kasa da kasa na 'yancin bil'adama.