Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makomar Wasu Cibiyoyin Kudi Ta Sa Manyan Kasuwannin Saida Hannayen Jarin Duniya Zuna Zubar Gado Daya Bayan Daya


Manyan kasuwannin saida hannayen Jari na Duniya suna zubar gado, daya bayan daya a yau litinin,saboda fargabar matsalar kudi da ake fiskanta zai kara durkusad da wasu cibiyoyin kudi.

Kokari da shugabnnin kasashen Duniya suke yi da nufin dakile faduwar da kasuwannin saida hannayen jarin baya tasiri,har ma wasu masu zuba jari suna kiran yinin yau “Bakar Litinin”. Manyan kasuwannin shunkun Turai sunyi mummunar hasara da basu taba irin ta ba a yini daya,yayinda kasuwar saida hannayen jari ta Japan,tayi faduwar da ba a ga irin ta cikin shekaru hudu da suka wuce.

Brazil ta dakatar hada-hadar kasuwar saida hannayen Jarin ta bayan da ta fadi da fiyeda kashi 10,yayinda jami’an Rasha suka ce kasuwar saida hannayen jarin kasar tayi hasarar da bata taba irin ta ba a yini daya.

A Amurka,kasuwar saida hannayen jari Dow Jones, ta fadi fiyeda kashi 500,kasa da dubu 10, a karo na farko cikin shekaru 4. Fargabar makomar tattalin arziki baki daya ya sa farashin danyen mai ya fadi zuwa dala 90 kan ko wace ganga a cinikin yau a kasuwar New York,watanni takwas rabon da a saida mai kan wannan farashi.

Shugabannin Turai sunyi kokarin sake karfafa masu zuba jari gwiwa,suna masu cewa a yau zasu dauki dukkan matakada suka wajaba wajen daidaita kasuwannin saida hannayen jari.

XS
SM
MD
LG