Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashewar Bututun Man Fetur Ta Kashe Daruruwan Yan Najeriya


Jami’an kungiyar agaji ta Red Cross a Najeriya, sunce daruruwan mutane ne suka mutu a wani hatsarin fashewar bututun man fetur, da ya faru a birnin Ikko. Kungiyar ta Red Cross tace Litinin dinnan bututun ya fashe a kauyen Adule Egba.

Akwai alamun cewa wadanda hatsarin ya rutsa dasu sunje ne suna diban mai daga bakin wani bututu da barayin mai suka fasa a daren Lahadi, kafin ya kama da wuta.

Har yanzu dai ba ba tantance ko mutum nawa ne suka rasa rayukansu ba, amma dai wadanda suka ganewa idanunsu abin da ya faru, sunce sunga daruruwan gawawwaki birjik, ga kuma wasu nan da wuta taiwa munanan raunuka suna ta murkususu. Harshen wutar, wanda ya mamaye yankin, yana kawo cikas wajen aikin ceto.

Hadurran fashewar bututun man fetur sun sha kashe dimbin mutane a Najeria, musamman ma ga wadanda kan garzaya wajen da bututun ya fashe su rika tarar man dake kwarara a cikin jarkoki, garewani da galalluka.

Wanna fashewar ita ce ta takwas a sassa dabam-dabam na Najeriya cikin kasa da shekaru goma. An taba kwata irin wannan a watan Octoban shekarar 1998, lokacin da fashewar bututun mai ta rutsa da dubban mutane a kauyen Jesse, a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur. Haka kuma a watan Yunin shekara ta 2003, sama da mutum 300 ne suka hallaka, a wani hadarin a wannan yanki.

XS
SM
MD
LG