Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kwango Laurent Kabila Ya Kori Babban Hafsan Mayakan Kasar,Dakarunsa Suna Ci Gaba Da Shan Kashi A Hanun 'Yan Tawaye.


Shugaba Joseph Kabila, na Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango,ya maye gurbin shugaban rundunar mayakan kasar,yayin da dakarunsa suke ci gaba da fama kan 'yan tawaye dake ci gaba da dannowa a wani lardin kasar dake gabashi.

A yammacin jiya Litinin ce,shugaba Kabila ya kori Lt.Janar Dieudonne Kayemba,ya maye gurbinsa da Lt.Janar Didier Etuma. Gidan radiyo da Majalisar Dinkin Duniya yake gudanarwa da ake kira Okapi,yace sabon hafsan mai shekaru 53 da haifuwa,ya sami horon soji a Brussels,kuma ya taba rike mukamin babban hafsa mai kula da harkar mulki na sojojin ruwan Kwango. Dakarun Gwamnatin kasar suna shan kashi a hannun 'yan tawayen dake karkashin bijirarren janar Laurent Nkunda,tun sa'adda 'yan tawayen suka kaddamar da farmaki a lardin Kivu ta Arewa cikin watan jiya.

Yau Talata,sojojin Gwamnati sun kara da mayakan sa kai kusa da garin Kanyabayonga. Madugun mayakan sa kai Sikuli Lafontaine, ya gayawa manema labaru cewa Dakarun sun kai hari kan mazauna kauyuka,suka kwashi ganima,bayan arangamar da suka yi dasu.

XS
SM
MD
LG