Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gaddafi Yayi Alkawarin Shawo Kan ‘Yan Tawayen Darfur


A ranar Asabar Mr Ban ya shaidawa manema labarai cewa yana da kyakkyawan zaton cewa Shugaba Muammar Gaddafi zai taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar taron, wanda za a bude a Libya ranar 27 ga watan gobe.

Mr. Ban ya gana da Shugaban na Libya a gidansa dake Sirte, kimanin kilomita 450, Arewa maso Gabashin babban birnin kasar, Tripoli. Sakatare Janar din yace kungiyoyin ‘yan tawaye da dama sun amince da Gaddafi, wannan kuma zai taimakwa nasarar taron na watan October.

Mr Ban ya karasa Libya ne daga Chadi, inda Shugaba Idriss Deby ya bada tayin gudanar da taron share fage da kungiyoyin tawaye, kafin taron na Tripoli.

Rabe raben kawuna tsakanin ‘yan tawayen shine babbar matsalar dake hana yinkurin kawo zaman lafiya samun nasara a yankin na Darfur.

XS
SM
MD
LG