Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadarin Motar Dakon Mai Ya Kashe Mutane Ashirin Da Biyar A Ghana.


Shaidun gani da ido a Ghana sun bada labarin mutuwar mutane ashirin da biyar,bayan tankar mai ta yi bindiga.

A yau laraba ce lamarin ya auku a garin Techiman dake tsakiyar kasar,mai tazarar kilomita 400 ta arewa maso gabashin fadar kasar Accra.

Shaidun sunce tankar ta yi bindiga ne bayan ta yi hadari.Wadanda suka halakan mutane ne da suka je dibar mai. Manema labaru da suke inda aka yi hadarin sun bada labarin cewa gawarwakin sun kone ta babu yadda za a gane su.

XS
SM
MD
LG