Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Rwanda Ta Tsayawa Janar Dinta


A Gwamnatin Rwanda tana kare wani janar dinta na soja, wanda ake zargi da keta hakkin dan adam, wanda aka zaba ya kasance mataimakin kwamandan rundunar Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tariyar Africa a Darfur.

Kungiyar ‘yan gudun hijirar Rwanda, wacce aka fi sani da Inkingi, sun zargi Janar Karenzi Karake da jagorantar kashe mutanen da basu ji ba, basu gani ba, kafin, da kuma bayan kisan kare dangin Rwanda, da kuma shirya kashe-kashen dimbin ‘yan siyasa.

A wata sanarwa da suka bayar jiya Talata, Ma’aikatar Harkokin Wajen Rwanda tace Janar Karake ya sami kwararren soja ne da ya sami cikakken horo, wanda kuma ya chanchanci wannan mukami.

Ma’aikatar tace wadannan zarge zarge, kage ne kawai, a kokarin wadansu mutane na bata sunan gwamnatin Rwanda, da kuma ruda kasashen duniya.

Majalisar Dinkin Duniya tace tana binciken wadannan zarge zarge.

XS
SM
MD
LG