Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Indiya Sun Gano Gawarwakin Mutane Da Aka Yi Garkuwa Da SuJami‘an tsaro a ƙasar Indiya sun bada rahoton cewar an gano gawarwaki biyar ta waɗanda ’yan bindiga ke garkuwa dasu gidan ibadar Yahudawa na Chabad dake Mumbai cibiyar cinikayyar Indiya.

A tattaunawar da gidan Telbijin na Indiya yayi dashi ɗazu da Maghriba, Dareta Janar na rundunar tsaron Indiya J.K. Dutt bai bayyana dalla-dallar daga ƙasashen da waɗanda ake garkuwa dasu suka fito ba, amma yace jami‘an tsaron Indiya sun kashe ’yan bindiga biyar a gidan na Chabad.

XS
SM
MD
LG