Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Isra'ila Ya Kasa Raunana Rokokin Hamas


Yau an ci gaba da gumurzu tsakanin Kungiyar Hamas da dakarun Isra’ila a Zirin Gaza, yayin da aka shige kwana na goma, Isra’ila tana kai munanan hare-haren ta sama.

A yau Ministan Tsaro Ehud Barack yace yakin zai ci gaba har sai Isra’ila ta tabbatar da cewa Yahudawa mazauna yankin gabashin Isra’ila sun tsira daga hare-haren rokoki daga Hamas.

Duk da wannan luguden wta daga sama, ‘yan hamas sun ci gaba da harba rokoki cikin Isra’ila, inda har suka kashe yahudawa hudu.

Ma’aikatan lafiya a Zirin Gaza sunce kimanin Falasdinawa 530 ne suka mutu cikin kwanaki goman, ciki har da a kalla farar hula goma sha daya, da kananan yara biyar.

Isra’ila tace sojan ta daya ya mutu tun daga liokacin da dakarunta na kasa suka shiga Zirin Gaza, an kuma raunata wasu guda talatin.

XS
SM
MD
LG