Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattijan Amurka Zata Yi Muhawara  Kan Daftarin Ceto Tattalin Arzikin Kasar


A daren Laraba ake sa ran Majalisar Dattijan Amurka zata kada kuri’a kan daftarin shirin ceto cibiyoyin kudin Amurka da akayiwa kwaskwarima na dala milyan dubu dari bakwai da Majalisar wakilai tayi fatali da shi ranar litinin.

Ana sa ran shirin zai kunshi tanadin kara kudin lamunin inshora da Gwamnati take yi kan ajiyar banki daga dala dubu dari zuwa dala dubu metan da hamsin.Haka kuma shirin zai kunshi rangwamen haraji ga mutane da kamfanoni,ciki harda rangwamen amfani da wasu hanyoyin samarda makamashi,kamar iska da rana.

Ahalin yanzu kuma,kasuwannin shunku a Asiya da Turai sun cira sama a hada hadar yau Laraba,saboda kyakkyawar fatar da masu zuba jari suke dashi cewa Majalisar dokokin Amurka zata amince da gagarumin daftarin ceto cibiyoyin kudin Amurka. Kasuwar saida hannayen Jari Nikkei na Japan yayi ribar maki dari 108.

Haka kuma hannayen jari a kasuwannin shunku Sydney,Taipei da Wellington duk sun cira sama. Akasarin kasuwannin Asiyan duk suna rufe saboda hutu. Haka kuma hannayen jari a London,Paris, da Jamus duk sun haura a hada hadar a farkon yinin yau.

Farashin mai ma ya tashi a cinikayyar farko farko a yau Laraba.
XS
SM
MD
LG