Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Huckabee Da Obama Sun Tsallake Siradi Na Farko


Tsohon Gwamnan Jihar Arkansa, Mike Huckabee, da Sanata Barak Obama sun lashe zagayen farko na zaben fid da gwani na Jam’iyyaunsu a Iowa, duk da cewar ba su aka sa ran zasu ci ba.

Shi dai Dan Majalisar Dattawa daga Jihar Illinois, Barak Obama, shine ke fafutukar zama bakar fata na farko da zai dare kujerar shugabancin Amurka. Sanata Barak Obama, ya shaidawa magoya bayansa, bayan an baiyana nasararsa cewa, mutanen Iowa sun zabi fata na gari a maimakon tsoro, sun zabi hadin kai maimakon rabuwa, sun kuma aike da sakon neman sauyi.

Tsohon dan Majalisar dattawa John Edwards shine ya zo na biyu, ita kuma uwar gidan tsohon Shugaban Kasa Bill Clinton, wato Hilary Clinton, wadda take kan gaba a zabukan jin ra’ayin jama’a, sai gashi ta zo ta uku.

Masu kada kuri’a a wannan ‘yar karamar jiha, sun bijirewa tsananin sanyin da ake fama da shi, inda suka yi tururuwa zuwa wajen tarukan, suka kuma zabi mutanen da suke fatan zasu kaiga wakiltar jam’iyyunsu.

Jam’iyyar Republican zata gudanar da wani zagayen zaben gobe Asabar a jihar Wyoming, sannan jam’iyyun biyu su sake haduwa a Jihar New Hempshire inda zasu sake gudanar da zabukan fidda gwaninsu a wannan jihar ranar Talata ta makon gobe.

Daga nan kuma jihohi zasu yi ta gudanar da nasu zabubbukan a ‘yan watannin nan masu shigowa. A Watannin Agusta da Satumba jam’iyyun biyu zasu gudanar da manyan tarukansu na kasa, inda ko wacce jam’iyya zata ftar da dan nata takarar da zai tsaya mata a babban zaben watan Nuwamba.

XS
SM
MD
LG