Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Pakistan Sun Kara Zafin Mulkin Kama Karya


Daruruwan magoyta bayanta sun taru a kofar ghidanta na Lahore, cikin shirin taka saiyada tun daga nan har zuwa birnin Islamabad.

An watsa yawancinsu cikin motocin ‘yan sanda da ake yiwa lakani da shiga da kai, fita da hawaye, inda aka kaisu gidan wakafi. Ita kuwa daga cikin gidan da take kulle, Mrs. Bhutto ta bukaci Shugaba Musharraf ta sauka daga kan mukaminsa na shugaban kasa, kuma ya tube masu kakinsu na soja.

Wannan shine karon farko da take neman kira sugaba Musharraf ya sauka kwata-kwata daga mulki. A ‘yan watannin baya shugabannin biyu suka gana, a inda suka cimma wata yarjejeniyar rabon mukamai da Amurka ke goyon baya.

Amma Mrs. Bhutto tace ganin yadda Shugaba Musharraf yake amfani da karfin tuwo a ‘yan kwanakin nan da ya ayyana dokar ta baci, ba zata iya zama Prime Minista a karkashin mulkinsa ba.

Ta ma yi barazanar hade guiwa da tsohon Prime Minista Nawaz Sharif.

XS
SM
MD
LG