Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asusun Bada Lamuni(IMF),Yace Tattalin Arzikin Kasashe Da Dama Suna Fuskantar Barazana


Asusun lamuni da bada rance na ƙasa da ƙasa, IMF ya bada rahoton cewar tattalin arzikin ƙasashe da dama a duniya sun fuskanci barazana saboda matsalar rikicin kasuwannin hannayen jarin da ake ƙoƙarin kaudawa.

Rahoton da Asyusun na IMF ya bayar yau Alhamis na bayanin cewa har yanzu tattalin arzikin ƙasa da ƙasa na tafiyar Hawainiya, ƙasa da kashi biyar daga cikin ɗari na hauhawar da ya kamata a samu a dai dai wannan lokaci. Rahoton na Asusun IMF yace nan zuwa shekara mai zuwa su kansu tattalin arzikin ƙasashe masu arzikin masana’antu zai fuskanci barazana ganin yadda a yanzu yake ɗigirgire, kuma waɗanda zasu fi cutuwa sune Amurka da ƙasashen Turai.

Kazalika itama China tattalin arzikinta zai ɗan yi ƙasa da kashi goma daga cikin ɗari a wannan shekarar, amma zai sake daɗowa zuwa kashi takwas da rabi daga cikin ɗari a shekarar 2009.

XS
SM
MD
LG