Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

India Ta Harba Kumbo Zuwa Duniyar Wata


India tayi nasarar harba jirgin kumbo zuwa doron wata da ake sarrafashi daga kan doron kasa. Jami’an India sunce kumbon da aka lakabawa sunann Chandarayan na farko,sunce a farkon yinin Laraban nan ne aka harba jirgin daga tashar dake Sriharikota,dake kusa da birninChennai.

Shugaban hukumar binciken sararin samaniya ta India,Mr. Madhavan Nair,ya kira harba kumbon takun farko kan wannan aiki dake da muhimmanci. Ya gayawa manema labaru cewa shirin yana tafiya kamar yadda ya kamata,yayinda masana kimiya dake kallon tashin kumbon ta talabijin,sunai sowar wannan nasara.

Jami’an India sunce Kumbon da zai tsaya kan doron wata na shekaru biyu zai dauki taswirar wata da kuma abinda ke karkashisa,wajen yin amfani da sabbin na’urorin zamani a karo na farko.

XS
SM
MD
LG