Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Kai Farmaki Kan Sansanonin Yan Tawayen Kurdawa a Iraki


Jami’an Iraqi sunce Sojojin Iran sun harba bindigogin egwa kan wasu kauyuka da suke zaton mafakar yan tawayen kurdawa.

Jami’an sukace sojojin Iran, sunyi luguden wuta kan kauyukan dake lardin Sulaimaniyah dake kusa da kan iyaka da Iran na tsawon sa’a daya a yau Alhamis. Babu rahoton jikkata,amma jami’ai sukace kauyawa sun firgita. Farisa bata gaskanta labarin harin ba.

Jami’an Iraqi sunce bisa dukkan alamu sojojin Iran sun auna harin ne kan sansanonin kungiyar ‘yan tawayen kurdawa da ake kira kungiyar da’awar enci da rayuwa ta kurdawa, ko PJAK a takaice.Iran tana aza laifin munanan hare hare a arewacin kasarta kan ‘yan tawayen wannan kungiya.

Jami’an Iran sunce dakarunta sun kashe ‘yan tawayen da dama a fada da suka gwabza jiya Laraba,a lardin Kordestan dake arewa maso yammacin kasar.Jami’an sun zargi ‘yan tawayen da kokarin hana zaben shiga Majalisar kasar da za’ayi Jummaa.

XS
SM
MD
LG