Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Boma Bomai Uku Sun Kashe Akalla Mutane Goma Sha Tara A Iraqi.


Rundunar ’yan sandan Iraqi ta bada rahoton cewa aƙalla mutane goma sha tara ne suka halaka a dalilin tashin boma-bomai a wurare uku a birnin Bagadaza.

Bom na farko ya tashine a dai dai lokacin da mutane ke zuwa wuraren ayukansu dasafe, mutane goma sha uku ne suka hakala, bom na biyu kuma ya tashi a kusa da wata ƙaramar motar safa dake ɗauke da ma’aikata zuwa wajenaikinsu kusa da ma’aikatar cinikayya.

Ɗaya bom ɗin kuma na gafen titi ne ya tashi yayin da motocin ke wucewa. ’Yan sandan suka ce mutane aƙalla biyar sun jikkata.

XS
SM
MD
LG