Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Siyasar Ivory Coast Sun Fara Taro Domin Tattaunawa Kan  makomar Zaben Kasar Da Ake Yawan Jinkirtawa


Shugabannin siyasar ƙasar Ivory Coast sun fara tattaunawa a Burkina Faso domin tsara sabon wa’adin shirya babban zaɓe a ƙasar Ivory Coast da ake yawaita jinkirta yinsa.

Tun farko an shirya gudanar da babban zaɓen ne a ran Talatin ga wannan watan na Nuwamba, amma sai aka bada sanarwar sake jinkirta yin zaɓe saboda wata matsalar da ta taso ta kayan aiki da rashin sabuwar rajistar masu zaɓe.

Shugaba Blaise Compaore na Burkina Faso ke jagorancin zaman taron na yau litinin, sannan shugaba Laurent Gbagbo da friministan Ivory Coast Guillaume Soro tare da jagoran ’;yan hamayya Henri Konan Bedie ke halarta tare da Alassane Outtara. Majalisar Dinkin Duniya tace tayi kiran da a gudanar da zaɓen majalisar dokoki da na shugaban ƙasar Ivory Coast a watan Yunin shekarar 2009.

XS
SM
MD
LG