Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jacob Zuma Ya Lashe Zaben ANC A Afirka Ta Kudu


Jam’iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta Kudu, ta zabi tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Jacob Zuma a matsayin Shugabanta, inda suka yi waje da Shugaban Kasa Thabo Mbeki daga kan wannan matsayi.

Zuma ya sami kuri’u 60, shi kuma Zuma yana da 40, a babban taron jam’iyyar da aka gudanar a jiya Talata. Wannan mukami ya sanya Zuma a zai iya kasancewa Shugaban kasar, idan har ANC ta lashe babban zaben kasar da za a gudanar a shekara ta 2009.

Wannan nasara ta Zuma, ta sanya magoya bayansa sun barke da sowa ta murna. Magoya bayan zume, sune kuma suka lashe dukkan manyan mukaman jam’iyyar guda biyar, bayan na Shugaban.

Wannan zabe ya fito da matsananciyar adawa da rarrabuwar kawunan dake cikin jam’iyyar ta ANC, wacce ke mulkin Afirka ta Kudu, tunda aka kawo karshen mulkin wariyar al’umma a shekarar 1994.

XS
SM
MD
LG