Jaridar New York Time ta bada labarin cewa jami’an leken asirin kasar Pakistan da kuma na Amurka sun kama babban kwamandan mayakan Taliban kwanakin da suka shige a wani sumame da suka kai birnin Karachi a asirce.
Jaridar ta bada labarin cewa jami’an gwamnatin Amurka wadanda suka ce kwamanda Mullah Abdul Ghani Baradar, yana hannun gwamnatin kasar Pakistan. An bayyana shi a matsayin na biyu a matakin iko biye da Mullah Muhammad Omar wanda ya kafa kungiyar Taliban. Baradar dan asalin kasar Afghanistan ne.
Jami’an da jaridar The Times ta ambata sun bayyana shi a matsayin dan kungiyar taliban mafi muhimmanci da aka kama tunda aka fara yakin Afghanistan karshen shekara ta dubu biyu da daya. Kungiyar Taliban a Afghanistan ta musanta kamashi ta bayyana rahoton a matsayin jita-jita kawai da ake yayatawa da nufin dauke hankalin jama’a.