Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Hamayya A Zimbabwe Tace Baza Taje Zagayen Zabe na Biyu Ba


Babbar Jam’iyyar Hamayya ta Zimbabwe, tace Shugabanta Morgan Tsvangirai ba zai shiga zagaye na biyu na babban zaben kasar ba.

Sakater janar na Jam’iyyar MDC, Tendai Biti yace Jam’iyyarsu ita ce ta lashe zaben 29 ga watan Maris, koda yake Hukumar Zaben kasar tace bata kammala hada alkaluman zaben ba.

Saidai yace Jam’iyyar zata halarci taron gaggawa na Shugabannin Kasashen Kudancin Africa, wanda aka kira a birnin Johannesburg na Africa ta Kudu, domin tattauna matsalar ta Zimbabwe.

Yace suna fata taron na Shugabannin Kasashen Kudancin Africa, zai mikawa Shugaba Mugabe wani sako mai gauni, cewa ya Shugaba, ka bada gudunmawarka ga wannan kasa, yanzu ka zama uba, ka sauka salin alin ka baiwa zabin jama’a dama ya gwada irin tasa basirar.

Amma Ministan Shari’a Patrick Chinamasa yace Jam’iyyar ZANU-PF ta Shugaba Mugage, so ma take a sake kidaya kuri’un da aka kada, saboda ta gano wasu kurakurai da aka tafka wajen kidayar.

Yace Wasu daga cikin kura kuran sa iya zama ajizancin dan adam, wasu kuma sa iya kasancewa ta’asa da aka tafka da gangan, daga mutanen da basa so a sami sakamako na gaskiya.”

XS
SM
MD
LG