Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jikin Fidel Castro Yayi Tsanani


Hukumomin Kasar Andalusiya ko Spain sun tabbatar da cewa wani kwararren likitan kasarsu ya tafi Cuba domin duba Shugaba Fidel Castro, wanda ke fama da jiki.

Kafofin yada labarai sun bada labarin isar Jose Luis Garcia Sabrido, zuwa birnin Havana, domin ya duba ko akwai bukatar a sake yiwa Shugaba Castro karin aikin Tiyata.

Shugaba Castro dai yana kwance, tun da aka yi masa wani aiki a hanjinsa a watan Yunin da ya gabata. Tun daga lokacin ne ya mika ragamar shugabancin kasar ga kaninsa Raul, kuma ba a sake ganinsa a bainar jama’a ba.

Jami’an Cuba sun karyata cewar cutar Sankara ce ke damun shugaban, har suka fito da hotuna da fina-finan video nasa. Amma dai wani jami’in leken asirin Amurka, John Negroponte yace Shugaba Castro na cikin wani matsanancin hali, kima zai iya mutuwa nan da ‘yan watanni.

XS
SM
MD
LG