Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Litinin,Shugaban Amurka Mai Jiran Gado Barack Obama,Yana Ganawa Da Abokin Hamayyarsa A Zaben Shugaban Kasa, John McCain.


Shugaban Amurka mai jiran Gado Barack Obama a yau litinin ya gana fuska dafuska da abokin takararsa a zaɓen shugaban ƙasa John McCain.

Shugaba mai jiran gado Obama yace maƙasudin ganawar shine neman haɗin kan Mccain game da yadda za’a kafa sabuwar Gwamnatin Amurka mai inganci. Mr.Obama yana mai ƙarfafa cewar yana buƙatar ganin yayi aiki tare da ’yan Democrat da Republican domin gano hanyar warware matsalolin dake addabar Amurka.

A tattaunawar da aka yi dashi jiya a gidan Telbijin na CBS, shugaba mai jiran gado Barack Obama yace zai yi iyaka ƙoƙarinsa domin farfaɗo da tattalin arzikin Amurka, da maido da martabar Amurka a idanun duniya tare da ƙoƙarta samar da ayyukan yi ga Amerkawa.

XS
SM
MD
LG