Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lamura Sun Fara Daidaituwa Jos Fadar Jihar Plateau, A Najeriya.


Rahotanni daga Nigeria na cewa al’amura sun yist a Jos, babban birnin jihar Plataeu Nigeria bayan kwanaki biyun da aka yi ana rikicin da ya janyo asarar rayukan mutane masu tarin yawa.

Shaidun gani da ido sun bada labarin cewar an sake bubbuɗe shagunan cinikayya yau litinin, sannan mutane sun fara fita zuwa sayayyar kayan masarufi, sai dai har yanzu soj ne ke sintiri a kan titunan birnin Jos domin tabbatar da ganin ana aiki da dokar hana yawon daren da aka kafa. A wasu unguwannin sasan Josdokar hana yawon na aiki har tsahon sa’o’i 24 saboda ƙazancewar al‘amura a unguwannin.

Jiya lahadi kwamishinan labarai Nuhu Gagara ya bada ƙididdigar cewa mutanen da suka halaka a dalilin rikicin sun kai metan, amma jami‘an lafiya sun ce da alamar adadin zai haura haka.

XS
SM
MD
LG