Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Juma'ar Nan Ake Ci Gaba Da Taron Daunin Iko A Zimbabwe


Jam’iyyar hamayya ta Zimbabwe, tace tattaunawar da suke da jam’iyya mai mulki domin kafa gwamnatin hadin guiwa ta cije, amma dai za a ci gaba da tattaunawa a yau Juma’a.

Kakakin Jam’iyyar Hamayya ta MDC, Nelson Chamisa yace jam’iyyarsu ta bukaci mai shiga tsakani, kuma tsohon Shugaban Afirka ta kudu, Thabo Mbeki da ya samo wata sahihiyar hanyar warware dambarwar dake tsakaninsu.

Shugaba Robert Mugabe ya baiyana kyakkyawan zaton cewa za a sami mafita, amma dai yace tilas sai dukkan bangarorin masu hamayya sun sadaukar da kai, kafin a iya tsinana wani abu.

Tattaunawar dai ana yinta ne tsakanin Shugaba Mugabe, da Shugaban Babbar Jam’iyyar Hamayya, Morgan Tsvangirai da kuma shugaban wani bangare na jam’iyyar adawar, Arthur Mutambura.

A ranar Lahadin da ta gabata Morgan Tsvangirai yayi barazanar janyewa daga tattaunawar, kwana daya bayan Shugaba Mugabe yayi gaban kansa, ya kuma nada mutanen jam’iyyarsa a ma’aikatu masu muhimmanci, cikinsu har da na tsaro da harkokin kasashen waje.

XS
SM
MD
LG