Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afirka Na Son Rage Bazuwar Kananan Makamai


Jiya Lahadi kimanin jami’ai 150 daga daga Kungiyar Gamayyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma, wato ECOWAS suka kammala wani taro na kwana biyar a Accra ta kasar Ghana.

Wanda ya Shugabancizama na karshe na wannan taro, Conmany Wasseh, wanda har ila yau shine Shugaban Hukumar Kula da kananan Makamai ta Kasar Liberiya, yace taron ya tattauna yadda za a sa ido kan bazuwar irin wadannan makamai.

Ya lura da cewa yawancin makaman daga wajen Afirka suke zuwa, ya kuma jaddada muhimmancin fadakar da jama’a kan bukatar gano da kuma kai rahoton irin wadannan makamai.

A watan Yunin bara ma, shugabannin yankin sunyi wani taro kan kananan makamai. Saidai tilas sai a kalla kasashe tara, daga cikin 15 dake da wakilci a kungiyar sun sa hannu kafin kudurin ya iya yin wani tasiri. Ya zuwa yanzu dai Jamhuriyar Nijar ce kadai ta rattaba hannu a kan kudurin.

XS
SM
MD
LG