Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hannayen Jari A Kasuwannin Turai da Asiya Sun Yi Kasa A Hada-Hadar Yinin Talata


An sami koma baya yau a manyan kasuwannin ƙasashen turai da kuma Asiya, yayin da ake ɗari ɗari kan faɗuwa da za a samu duk da maƙudan kuɗin da ƙasar China ta ware domin rage zafin matsin da koma bayan tattalin arziki ya haifar.

Kasuwannin hannayen jari a Tokyo da Taipei da Sydney sun faɗi bayan da kamfanoni da dama da suka haɗa da Toyota da Citizen-kamfanin agogo mafi girma a duniya, suka sanar da cewa riba da suke samu ta ragu ainun. Kasuwannin hannayen jari a turai sun faɗi da kashi 2% yau da rana.

Masu zuba jari sun kuma bayyana damuwa da durƙushewar da kamfanin Circuit City na Amirka ya yi- kanfanin saida na’urorin lantarki na biyu mafi girma a amurka. Masu kula da lamura kuma sun bayyana yiwuwar samun faɗuwa a kamfanin ƙirar motoci na General Motors da kamfanin zuba jari na Goldman Sachs.

A wata alamar koma bayan tattalin arziki kuma, jami’an ƙasar China sun ce bukatar shigowa da kayayyakin ƙetare ya ragu a watan Oktoba abinda ya haddasa samun kwantan kayyaki na kimanin dala miliyan dubu talatin da biyar.

XS
SM
MD
LG