Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Kasuwannin Hannayen Jarin Duniya Sun Fara Farfadowa


Farashin hannayen jari a kasuwannin Duniya sun ɗaga sama a yau litinin saboda matakan da Gwamnatocin ƙasa da ƙasa ke ɗauka na ƙarfafa tasirin cinikayyar hannayen jari.

Alƙaluman cinikayyar hannyen jari a kasuwar London a sha biyun ranar litinin, sun ɗaga da kashi huɗu daga cikin ɗari, kazalika a kasuwannin hannayen jarin Paris da Frankfurt da suka yi sama da kashi shida daga cikin ɗari.

Ta ɓangaren cinikayyar lamuni kuwa kasuwannin Amurka sun nuna alamun fara murmurewa a kasuwar Wall Street. A can kasuwannin Asiya kuma alƙaluman hannayen jari sun lumfasa a Hong inda sukayi sama da kashi goma daga cikin ɗari.

XS
SM
MD
LG