Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Tsarin Mulki A Thailand Ta Rusa Gwamnatin Kasar.


PM ƙasar Thailand Somchai Wongsawat ya bayyana amincewa da hukumcin da kotun tsarin mulkin ƙasar ta yanke na dakatar da shi daga shiga harkokin siyasa na tsawon shekaru biyar da kuma rusa jam’iyarsa.

Da yake magana a birnin Chiang Mai na arewacin ƙasar, daga inda yake gudanar da harkokin mulki tunda masu zanga zanga suka mamaye manyan tashoshin sufurin jiragen saman ƙasar makon jiya, Mr. Somchai ya shaidawa manema labarai cewa aikinsa ya ƙare, yanzu daidai yake da kowanne ɗan ƙasa.

Yau kotun tsarin mulkin ƙasar Thailand ta umurci rusa manyan jam’iyun uku dake gwamnatin haɗin guiwa ta Mr. Somchai bisa zargin maguɗin zaɓe.

XS
SM
MD
LG