Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Soke Zaben Gwamna Na Hudu A Najeriya


A yau kotun ta yanke hukuncin cewa babu wata hujja da za a saka sunan Celestine Omeha na Jam’iyyar PDP a jerin ‘yan takarar gwamna, a zaben watan Aprilun da ya gabata.

Rotimi Ameachi, shima dan jam’iyyar PDP, shine ya lashe zaben fid da gwani na jam’iyyar, amma sai shugabannin jam’iyyar suka sa Hukumar Zabe ta musanya sunansa da na Omeiha a takardar kada kuri’a, jin kadan kafin zaben na watan Aprilu.

Kotun bada umarnin a rantsar da Amechi, wanda ya kai mata kukan wannan rashin adalchi da aka tafka masa, ba tare da wani bata lokaci ba.

Omeiha, Wannan shine gwamna na hudu da kotunan najeriya ke soke zabensu. Sauran sune na Jihohin Anambra, da Kogi da Kebbi wadanda aka soke a bisa dalilai mabanbanta.

Rahotannin daga Najeriya sunce a halin yanzu Gwamnoni da dama cikinsu ya duri ruwa, ganin har yanzu akwai gwamnonin da aka dora su a kan karagar mulki, ba tare da sun ci zabe ba.

Wasu ma ko zaben fid da gwani basu tsaya ba, kamar yadda tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.

XS
SM
MD
LG