Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Duniya Ta Bada Takardar Sammacin Shugaban Sudan


A ranar laraba, Kotun Kasa da Kasa mai hukunta manyan laifuffuka ta bayar da takardar sammaci a kan Shugaba Omar Hassan Albashir na Sudan, saboda laifuffukan yaki a yankin Darfur.

An dai tsananta tsaro a yankunan Sudan, inda ake tsamnmanin tashe-tashen hankula idan har kotun da bada sammacin.

Kotun tana tuhumar Albashir da laifuffukan kashe kashen kare dangi, da cin zarafin dan adam, da fyade a yankin Darfur na kasar Sudan.

Shugaba Albashir shine Shugaban kasa na farko a tarihi da za a kama a kan karagar mulki, tun da aka kafa kotun a shekara ta 2002, in dai har sammacin yayi tasirin kame shugaban.

Sudan tayi watsi da tuhume tuhumen da ake masa, ta kuma ce ba zata bada hadin kai ga kotun ba.

Zaman dar-dar ya kara yawaita a Sudan a yayin da daruruwan mutane suka hallara a babban birnin kasar na Khartoum domin gudanar da zanga zangar nuna fushinsu da wannan sammaci.

XS
SM
MD
LG