Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Alkaida Ta Kame wadansu Turawa A Jamhuriyar Nijar


Reshen al-Qaida na nahiyar Afrika ta Arewa yayi ikrarin cewa ya sace wasu jami'an diplomasiya biyu na Canada da wasu turawa hudu masu yawon shakatawa a Junhuriyar Nijer.

Tashar telebijin ta al-Qaida ce ta watso wannan sanarwar da aka ji tana fitowa daga bakin kakakin kungiyar al-Qaida din, Salah Abu Mohammed.

Mai maganar yace kungiyar tasu na da cikakken ikon yin abinda taga dama da wadanan turawan guda shidda dake hannunta ta aiki dashari'ar islama. Ya kuma ce sai nan gaba zasu bada sharuddansu na sako su.

Tun cikin watan Disamba dai nanzon Canada a can Nijer Robert Fowler da mataimakinsa Louis Guay suka salwance a bayan garin Yamai, yayinda a tsakiyar watan Janairun da ya gabata wasu turawa biyu na kasar Sweden, mace da namiji, hade da wata mace Bajamusa da kuma wani baturen Ingila suma suka bace akan iyakar Nijer-Mali.

XS
SM
MD
LG