Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kare hakkin Bil'adam Ta Human Rights Watch Tace Rikici Da Ya Biyo Bayan Zaben Kenya Zama Akayi Aka Tsara Tashe Tashen Hankula Da Suka Kai Ga Zubda Jini


Wani sabon rahoto daga kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights watch tace akasarin tashe tahen hankula da suka faru a Kenya bayan zaben kasar da ya jawo ta kaddama tsarasu akayi.

Rahoton ya zargi ‘yan siyasar Kenya,shugabannin na kananan hukumomi,da ‘yan kasuwa wajen kitsa hare hare da aka kaiwa kabilu da suke ja da su.

Haka kuma rahoton yace ‘Yan sanda sun nuna fin karfi,suka kuma kashe daruruwan mutane lokacin da suke tinkarar masu zanga zanga.

Tashe tashen hankula da suka biyo bayan zaben na cikin watan Disemba ya halaka fiye da mutane dubu daya,ya raba dubban daruruwa mutane da muhallansu.

XS
SM
MD
LG