Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kare hakkin Dan Adam Tace Da Sauran Gyara A Najeriya


Jami’in Binciken kungiyar, Chris Albin Lackey, wanda ya fitar da wani rahoto a Lagos jiya Talata, yace rashaw da tashe tashen hankula karuwa ma suka yi a kasar daga lokacin da sojoji suka saki madafun mulki a shekarar 1999.

Wadansu mazauna Ikko da suka yi magana da wakilin Muryar Amurka sunce basu yi mamakin jin wannan bayani ba. Wani da ya fadi ra’ayinsa ma shawara ya bayar a rika yanke hukuncin kisa kan mutanen da aka samu da laifin haddasa tashin hankalin siyasa, ko satar dukiyar kasa.

Rahoton yayi kira ga Shugaba Umar Musa ‘Yar Aduwa da ya kawo karshe fifita wadansu shafaffu da mai, ya kuma gaggauta aiwatar da sauye sauye.

Saidai wani mai magana da yawun Gwamnatin ‘Yar Aduwa ya karyata batun cewa ‘Yar Aduwa yana bada kariya ga wani tsohon gwamna wanda a halin yanzu ke fuskantar bincike daga ‘yan sanda Birtaniya.

Kakakin Gwamnatin ta Umar ‘Yar Aduwa ya bayar da wata sanarwa inda yace Shugaban ya amince da wata tawagar ‘Yan Sandan Birtaniya su ziyarci najeriya domin bincikar tsohon Gwamnat Jihar delta, James Ibori.

A jiya talata wata kotu ta kwace kadarorin Ibori, da kimarsu ta kai dollar miliyan 35, wadanda ake zargin kudin gwamnati aka sata, aka sayesu.

XS
SM
MD
LG