Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Taliban Ta bayar Da Wa’adi Na Karshe A Afghasnisatan


Yousuf Ahmadi ya gayawa kamfanonin dillancin labaran kasashen yammacin duniya ta wayar talho a jiya alhamis cewa har yanzu akwai sauran damar tattaunawa. Ya kuma ce sauran wadanda ake garkuwar da su na nan da rai har yanzu.

Gidan telebijin na CBS a Amurka ya buga a dandanlin shi na na intanat cewa daya daga cikin matan da ake yin garkuwa da su ta yi magiya, tana rokon a taimaka, a hirar da gidan telebijin din ya yi da ita ta wayar talho.

Matar da aka ce sunan ta Im Hyun-joo, ta ce wadanda ake yi garkuwar da su ba su da lafiya, sun galabaita kuma su na cikin wani hali mai tsananin muni.

A birnin Washington DC, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Sean McCormack ya yi nadamar mutuwar daya daga cikin ’yan ƙasar Koriya ta Kudun da ake yin garkuwa da su. Ya ce Amurka na goyon bayan gwamnatin kasar Koriya ta Kudu a ƙoƙarin da ta ke yi na neman tabbatar da ’ya’yan kasar sun koma gida lami lafiya.

XS
SM
MD
LG