Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan Kumbon Endeavour Sun Dakatar Da Tattaki A Duniyar Wata


Hukumar Binciken sararin samaniyar Amurka, wato NASA, tace ‘yan sama jannatinta sun dakatar da wani tattaki da sukan yi a duniyar wata, saboda daya daga cikinsu ya gano wata ‘yar kofa a rigarsa ta sulke.

NASA tace Rick Mastracchio ta gano wannan ‘yar bula ne, lokacin da suke sudduba sulken nasu kamar yadda sukan yi lokaci-lokaci idan sun fito tattakin.

Hukumar tace baya cikin wani hadari, amma dai masu kula da kai komon kumbon, suka ce a dakatar da tattakin, don rigakafi.

Kafin su koma cikin kumbon nasu, ‘yan sama jannatin sun kammala wani muhimmin aiki da ya saka dambar kafa wata tashar bincike a sararin samaniya. Sun sake wa wata na’urar karbar sakonni mazauni.

A nan kasa, Shugaban kula da wannan jigilar, John Shannon, yace wata ‘yar lotsewa a gefen kumbon da aka gano baya ya tyashi, ba zata yi wata barazana ga lafiyar ‘yan sama jannatin ba. Yace alamun farko sun nuna cewa kumbon endeavour zai dawo lafiya ba tare da anyi masa wani gyara ba.

XS
SM
MD
LG