Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahukuntan Pakistan Sun Saki Masu Zanga-Zanga


Jami’an Kasar pakistan sunce sun saki kimanin mutum dubu uku da dari hudu, wadanda aka tsare a karkashin dokar ta bacin Shugaba Pervez Musharraf.

A yau Talata Kakakin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida Jawad Iqbal Cheema ya bada wannan bayani, inda yace ragowar kimanin mutum dubu biyu dake hannu yanzu, suma za a sakosu nan bada dadewa ba.

Jim kadan bayan an sako mutanen, ‘yan sanda suka yi taho mu gama da masu zanga zanga da sukai biris da haramcin gwamnati. Ance a birnin Karachi an kame a kalla maneman labarai 140, wadanda ke wani gangamin yin tofin ala-tsine ga wata dokar gwamnati da ta takaita masu ‘yanci, tun da aka kafa dokar ta bacin a farkon watan nan.

A yau din kuma Hukumar Zaben Pakistan tace an tsaida takwas ga watan gobe na Janairu ta zama ranar da za a gudanar da zaben Majalisar Kasar. Jam’iyyun adawa sunce zasu kauracewa zaben, sai fa in gwamnatin kasar ta dawo da mulkin dimokradiyya, ta kuma dawo da alkalan kotun kolin da shugaba Musharraf ya kora.

A halin da ake ciki kuma, shugaba Musharraf yana Kasar Saudi Arabiya, inda ya ttauna na Sarki Abdallah da manyan jami’an gwamnatinsa. Tsohon Shugaban Pakistan din, wanda ke zaman gudun hijira a Saudi Arabiya, ya musanta bayanai dake nuna cewa yana shirin ganawa da Mr. Musharraf a lokacin wannan ziyara.

XS
SM
MD
LG