Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yiwuwa A Tafka Magudi A Zaben Kamaru


Babbar jam’iyyar adawa ta Kamaru tace tana sa ran cewa za’a tabka bala’in magudi a babban zaben wakilan majalisar dokokin kasar Kamarun da za’ayi ran Lahadin din nan mai zuwa.

Suma kusoshin diplomasiya da na kare hakkokin jama’a duk suna tababar idan za’ayi adalci a wannan zaben wanda ake jin karashenta ba ma abinda zaiyi illa kara karfafa Jam'iyya mai mulki ta CPDM, wacce a yanzun ma itace ke rike da kujeru 149 daga jimillar kujeru 180 na majalisar dokokin kasar.

Kusoshin jam’iyyar adawa ta SDF ne suka fito suna cewa wannan zaben ba za’a yi shi a cikin gaskiya da adalaci ba.

Suka ce gwamnatin ta riga ta gama shimfidar tafka magudin ta hanyar zaban wa’anda take baiwa katin zaben, ta kuma sauya taswirar Cameroon baki daya.

Sai dai madugun SDF din, John Fru Ndi yace kauracewa zaben ba zai sauya komai ba, saboda haka gara duk kowa ya shiga don a hana wa gwamnatin ta shugaba Paul Biya sakat.

Shi dai shugaba Biya na Kamaru tun 1982 yake kan karagar mulki, abinda yassa yake daya daga cikin shugabannin Afrika da suka fi dadewa suna mulki.

XS
SM
MD
LG